Alignment Visualization        
English – Hausa
December 10, 2025 at 19:01
       
Search
Bible
Sample: % orauto
Max:  
       
Script ualign.py version 0.0.8
By Ulf Hermjakob, USC/ISI

Old Testament:GEN  EXO  LEV  NUM  DEU  JOS  JDG  RUT  1SA  2SA  1KI  2KI  1CH  2CH  EZR  NEH  EST  JOB  PSA  PRO  ECC  SNG  ISA  JER  LAM  EZK  DAN  HOS  JOL  AMO  OBA  JON  MIC  NAM  HAB  ZEP  HAG  ZEC  MAL 
New Testament:MAT  MRK  LUK  JHN  ACT  ROM  1CO  2CO  GAL  EPH  PHP  COL  1TH  2TH  1TI  2TI  TIT  PHM  HEB  JAS  1PE  2PE  1JN  2JN  3JN  JUD  REV 
Apocrypha:TOB  JDT  ESG  WIS  SIR  BAR  1MA  2MA  MAN 
Chapters of ECC:1  2  3  4  5  6  7  8  9  10  11  12 


ECC 4:1     Alignment score: 0.254 → 0.275
Once again I thought about all the oppression that is done under the sun . And behold , the tears of oppressed people , and they had no one to comfort them ! Power was in the hand of their oppressors , and there was no one to comfort them !
Na sake yin tunani game da cutarwar da ke faruwa a ƙarƙashin rana . Duba kuma , hawayen mutanen da aka cuta
, babu kuma wanda zai ta'azantar da su ! Iko na hannun masu cutar da su , babu kuma wanda zai ta'azantar da su !


ECC 4:2     Alignment score: 0.251
So I considered those who are already dead
more fortunate than the living , who are still alive .
Sai na yi la'akari da cewa waɗanda suka mutu sun fi waɗanda ke da rai morewa , waɗanda har yau suna raye .
ECC 4:3     Alignment score: 0.213
However , more fortunate than both of them is the one who has not yet lived , the one who has not seen any of the evil acts that are done under the sun .
Duk da haka , wanda ya fisu dukka morewa shi ne wanda bai riga
ya rayu ba , wanda bai riga ya ga ayyukan muguntar da ake yi ba ƙarƙashin rana .
ECC 4:4     Alignment score: 0.318 → 0.349
Then I saw that every act of labor and every skillful work became
the envy of one 's neighbor . This also is vapor and an attempt to shepherd the wind .
Daga nan naga cewa kowanne aikata aiki da aikin ƙwarewa ya zama kishin maƙwabcin wa ni . Wannan shi ma turirin hayaƙi ne da yunƙurin kiwon iska .
ECC 4:5     Alignment score: 0.308 → 0.309
The fool folds his hands and does not work , so his food is his own flesh .
Wawa yana naɗe hannuwansa
kuma baya aiki , domin wannan abincinsa jikinsa ne .
ECC 4:6     Alignment score: 0.38
But better is a handful of profit with quiet work than two handfuls with the work that tries to shepherd the wind .
Amma gwamma riba kaɗan tare da aikin natsuwa da hannuwa biyu cike
da aikin ƙoƙarin kiwon iska .
ECC 4:7     Alignment score: 0.376 → 0.386
Then I thought again about more futility , more vanishing vapor under the sun .
Daga nan na sake yin tunani game da ƙarin aikin wofi , ƙarin turirin hayaƙi mai ɓacewa a ƙarƙashin rana .
ECC 4:8     Alignment score: 0.303 → 0.306
There is the kind of man who is alone . He does not have anyone , no son or brother . There is no end to all his work , and his eyes are not satisfied with gaining wealth . He wonders , " For whom am I toiling and depriving myself of pleasure ? " This also is vapor , a bad situation .
Akwai wani irin mutum da ya ke shi kaɗai . Bai da kowa , ba ɗa ko ɗan'uwa . Babu ƙarshe ga dukkan aikinsa , idanunsa ba su ƙoshi da neman wadata . Yana mamaki , " Domin wa nake wahala
ina hana wa kaina jin daɗi ? " Wannan ma turirin hayaƙi ne , al'amari marar kyau .
ECC 4:9     Alignment score: 0.255
Two people work better than one ; together they can earn a good pay for their labor .
Mutum biyu za su yi aiki fiye da ɗaya ; tare
za su sami biya mai kyau game da aikinsu .
ECC 4:10     Alignment score: 0.343 → 0.354
For if one falls , the other can lift up his friend . However , sorrow follows the one who is alone when he falls if there is no one to lift him up .
Domin idan ɗaya ya fãɗi , ɗayan zai iya ɗaga abokinsa . Duk da haka , baƙinciki na biye
da wanda ke shi kaɗai sa ' ad da ya fãɗi idan babu wanda zai iya ɗaga shi .
ECC 4:11     Alignment score: 0.531 → 0.532
If two lie down together , they can be warm , but how can one be warm alone ?
Idan biyu suka
kwanta tare , za su iya jin ɗumi , amma ta yaya ɗaya zai ji ɗumi shi kaɗai ?
ECC 4:12     Alignment score: 0.34 → 0.361
One man alone can be overpowered , but two can withstand an attack , and a three - strand rope is not quickly broken .
Za a iya fin ƙarfin
mutum ɗaya shi kaɗai , amma biyu za su iya yin tsayayya da hari , igiya uku a murɗe ba za su yi saurin tsinkewa ba .
ECC 4:13     Alignment score: 0.295 → 0.294
It is better to be a poor but wise youth than an old and foolish king who no longer knows how to listen to warnings .
Gwamma wani ya zama matashi talaka amma mai wayau da tsohon sarki wawa wanda ya daina
sanin yadda ake sauraron kashedi .
ECC 4:14     Alignment score: 0.416
This is true even if the young man becomes king from prison , or even if he was born poor in his kingdom .
Wannan gaskiya ne koda saurayin ya zama sarki daga kurkuku , ko kuma an haife
shi talaka a masarautarsa .
ECC 4:15     Alignment score: 0.206 → 0.238
I saw everyone who was alive and was walking around under the sun , along with a youth who was to rise
up to take his place .
Na kalli kowa wanda ya ke da rai kuma yana yawonsa a ƙarƙashin rana , tare da matashin da ke tasowa ya maye gurbinsa .
ECC 4:16     Alignment score: 0.473 → 0.474
There is no end to all the people who want to obey the new king , but later many of them will no longer praise him . Surely this situation is vapor and an attempt to shepherd the wind .
Babu ƙarshen dukkan mutanen da suke
so suyi biyayya da sabon sarki , amma daga ba ya yawancin su ba zasu sake yabonsa ba . Tabbas wannan al'amari turirin hayaƙi ne da yunƙurin kiwon iska .
ECC 4:17     Alignment score: 0.353
Guard your steps when you go to the house of God . Go near to listen rather than to offer the sacrifice of fools , who do not understand that they are doing what is wrong .
Ka kiyaye takawarka sa ' ad da ka je gidan Allah . Ka matsa kusa ka saurara
fiye da miƙa hadayar wawaye , waɗanda basu fahimci cewa suna yin abin da ba dai - dai ba .
ECC 4     Average alignment score: 0.338 for 17 sentences.     Evaluation statistics page

Old Testament:GEN  EXO  LEV  NUM  DEU  JOS  JDG  RUT  1SA  2SA  1KI  2KI  1CH  2CH  EZR  NEH  EST  JOB  PSA  PRO  ECC  SNG  ISA  JER  LAM  EZK  DAN  HOS  JOL  AMO  OBA  JON  MIC  NAM  HAB  ZEP  HAG  ZEC  MAL 
New Testament:MAT  MRK  LUK  JHN  ACT  ROM  1CO  2CO  GAL  EPH  PHP  COL  1TH  2TH  1TI  2TI  TIT  PHM  HEB  JAS  1PE  2PE  1JN  2JN  3JN  JUD  REV 
Apocrypha:TOB  JDT  ESG  WIS  SIR  BAR  1MA  2MA  MAN 
Chapters of ECC:1  2  3  4  5  6  7  8  9  10  11  12